July 23, 2026

Hon Mubarak Abdullahi Gansy

Honourable Gansy Ya Yi Alƙawarin Samar da Ilimi Kyauta Idan Aka Zaɓe Shi Gwamnan Bauchi a 2027

Hon Mubarak Abdullahi Gansy

Ɗan takarar kujerar Gwamnan Jihar Bauchi na jam’iyyar African Action Congress (AAC), Honourable Gansy, ya yi alƙawarin samar da ilimi kyauta idan al’ummar jihar suka zaɓe shi a babban zaɓen shekarar 2027.

A cewarsa, ilimi shi ne ginshiƙin ci gaban al’umma, kuma gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen inganta makarantu, samar da kayan koyo, da tabbatar da cewa yara da matasa sun samu damar yin karatu ba tare da shingen kuɗi ba.

Ya kuma yi kira ga al’ummar Jihar Bauchi da su ba shi goyon baya domin aiwatar da manufofinsa na ci gaban ilimi da bunƙasa rayuwar al’umma.

— GASKIYA TV Muryar Jama’a

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *